A wajen bikin liyafar, firaminista Li Keqiang ya yi jawabin cewa, tun daga farkon shekarar bana, kasar Sin ta yi kokarin tinkarar wasu kalubalolin da ake samu, sakamakon sauyawar yanayi a ciki da wajen kasar, tare da samun ci gaba a fannin zurfafa gyare-gyare, da kara kokarin bude kofa ga kasashen waje, da kyautata huldar dake tsakaninta da kasashen waje, da karfafa hadin gwiwar da ake yi tare da sauran kasashe.
A cewar firaministan kasar Sin, kasar za ta tsaya kan manufar gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje, domin gyare-gyaren su ne dalilin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, kana irin ci gaban da ake samu, yana taimakawa wajen daidaita matsalolin da kasar ke fuskanta. (Bello Wang)