in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za mu manta da tarihi ba don gina kyakkyawar makoma
2018-09-30 16:57:37 cri
Yau Lahadi, 30 ga watan Satumban shekarar 2018, ranar ce ta tunawa da mutanen da suka yi shahada a kasar Sin karo na biyar. Gwamnatin kasar Sin ta shirya wani biki a gaban hasumiyar tunawa da jaruman kasar dake filin Tian'anmen na birnin Beijing don tunawa da wadannan shahidai wadanda suka rasa rayukansu a fafutukar neman 'yancin kan al'ummar kasar Sin da bunkasuwa da zaman wadatan kasar baki daya.

A halin yanzu, kasar Sin ta zaman babbar kasa mai samun saurin bunkasuwa a duniya. Kasashen duniya sun fara mai da hankali kan kasar Sin sakamakon babban ci gaba da ta samu cikin shekaru 40 da suka gabata ta hanyar bude kofa ga waje, abin da ya sa ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

A wannan lokaci na musamman, bai kamata mu manta da tarihin bacin rai da al'ummar kasar Sin suka taba fuskanta ba. A shekarar 1840, kasashen yammacin duniya sun kawo kasar Sin yakin da bai cancanta ba, sa'an nan, al'ummomin kasar Sin sun shafe kusan shekaru 100 na tashe-tashen hankula da bacin rai. Cikin wadannan shekaru, jarumai da yawa sun rasa rayukansu a yayin da suka bata kashi da abokan gaba domin kiyaye mutunci da 'yancin kasar Sin.

Sinawa suna ganin cewa, sun sami zaman lafiya sakamakon babbar gudummawar da jarumai masu dimbin yawa suka bayar. Domin tunawa da kuma nuna godiya ga wadannan jarumai, ya kamata su ci gaba dorwa kan ayyukan da suka fara domin gina al'umma mai kyakyyawar makoma da zaman lafiya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China