in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya ce kyakkyawar alaka tsakanin kasarsa da Amurka abu ne mai muhimmanci ga kasashen biyu
2018-09-26 10:33:14 cri

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kyakkyawar dangantaka tsakanin kasarsa da Amurka, na da muhimmanci gaya ga kasashen biyu da al'ummominsu da kuma zaman lafiya da ci gaban duniya.

Wang Yi ya bayyana haka ne yayin wani taro da wakilan kwamitin kasashen biyu dake kula da dangantaka da harkokin cinikayya a tsakaninsu, inda suka yi musayar ra'ayi game da batutuwan da suka shafi huldar kasa da kasa da na tattalin arziki da cinikayya.

Ya ce matakai marasa dacewa da Amurka ke dauka a baya-bayan nan kan kasar Sin na karuwa. Yana mai cewa wasu daga cikin matakan na dora laifi kan kasar Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya da tsaro, wadanda ke nuna son kai da kuma gurbata yanayin dangantakar kasashen biyu.

Ya kara da cewa, zarge-zargen da ake wa kasar Sin ba su da tushe, kuma idan ba a bincika ba, za su lalata nasarorin da dangantakar Sin da Amurka ta samu cikin shekaru 40 da suka gabata, wanda ya ce ba zai yi wa bangarorin biyu da ma duniya baki daya dadi ba.

Ya ce har kullum, kasar Sin kan yi kira da a warware duk wata matsala da ta kunno kai tsakaninta da Amurka bisa adalci da tattaunawa.

A nasu bangaren, wakilan kwamitin kula da dangantakar kasashen biyu sun ce kyakkyawar alaka tsakanin Sin da Amurka abu ne da zai amfani dukkan kasashen 2, inda suka ce cikin shekaru 40 da suka gabata, bangarorin 2 sun amfana sosai da huldar dake tsakaninsu.

Sun kuma bayyana cewa, galibin 'yan kasuwar Amurka ba su amince da warware matsalar da ake fuskanta bisa karawa juna haraji ba, sannan laifin da ake dorawa kasar Sin bai dace ba.

Bugu da kari, sun ce akwai bukatar Amurka da Sin su karfafa tattaunawa da juna, musammam a irin wannan lokaci, tare da kara fahimtar juna da warware matsalolinsu ta hanyar tuntubar juna. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China