in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da shaidu da matsayinta kan takaddamar cinikayya dake tsakaninta da Amurka
2018-09-24 13:52:40 cri
A yau Litinin ne, kasar Sin ta fitar da takardar bayani domin ta bayyana hakikanin shaidu game da alakar cinikayyar dake tsakaninta da kasar Amurka, ta kuma bayyana matsayin ta game da takaddamar cinikayyar dake tsakaninsu sannan ta dauki matakan da suka dace.

Baya ga gabatarwa, takardar mai sassan shida tana kunshe haruffan Sinanci 36,000 kuma dukkansu sun dace da moriyar juna kan alakar dake tsakanin kasashen biyu a fannin cinikayya da tattalin arziki, sannan sun bayyana hakikanin gaskiyar alakar Sin da Amurka a fannin cinikayya da tattalin arziki, da yadda gwamnatin Amurka ke ayyukan ba da kariya ga harkokin cinikayya, da yadda take saba harkokin cinikayya, da yadda tasirin lalata harkokin cinikayya da gwamnatin Amurkar ke yi ka iya shafar tattalin arzikin duniya da kuma matsayin kasar Sin.

Takardar bayanin ta bayyana cewa, kasar Sin babbar kasa ce mai tasowa a duniya yayin da kasar Amurka kuma babbar kasa ce da ta ci gaba a duniya. Alakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka na da muhimmanci ga kasashen biyu da ma zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.

Bugu da kari, takardar bayanin ta bayyana cewa, matsayin ci gaba da ma tsarin tattalin arzikin kasashen biyu ya bambanta, don haka, ba wani abu ba ne idan aka samu takaddamar cinikayya daga lokaci zuwa lokaci. Amma, abu mai muhimmanci shi ne, yadda kasashen biyu za su karfafa amincewa da juna, da bunkasa alakarsu da ma yadda za su warware bambance-babancen dake tsakaninsu yadda ya kamata.

Ko da yake tun lokacin da sabuwar gwamnatin Amurka ta kama aiki a shekarar 2017, take ikirarin kare martabar Amurka da farko, kana ta yi watsi da muhimman muradun mutunta juna da tuntubar juna daidai wa daida kamar yadda alakar kasa da kasa ta tanada.

Takardar bayanin ta kuma jaddada cewa, kasar Sin ta mayar da martani bisa la'akari da muradun dukkan bangarorin biyu da ma dokokin cinikayya na duniya, da martaba manufar warware takaddama ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna, da nuna hakuri da cikakken imani wajen amsa damuwar da Amurka ta gabatar

Har kullum bangaren kasar Sin, yana kokarin warware banbance-banbace bisa zurfin tunanin cimma daidato yayin yanke hukunci. Takardar bayanin ta kuma bayyana cewa, kasar Sin ta jure tarin wahalhalu da yin kokari matuka wajen daidaita alakar tattalin arziki da cinikayyar da Amurka ta hanyar shirya jerin tattaunawa da bangaren Amurka da ma tsara matakan magance lamarin a zahiri.

Daga karshen takardar bayanin ta bayyana cewa, bangaren Amurka ba ya tsayar da magana guda, sannan kullum yana ta kalubalantar kasar Sin.(IBrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China