in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karin haraji kan hajojin Sin ba zai kau da gibin cinikayyar Amurka ba in ji jimi'in Sin
2018-09-14 10:04:21 cri
Kakakin ma'aikatar cinikayya ta Sin ko MOC a takaice Mr. Gao Feng, ya ce matakin da Amurka ke dauka na karin haraji kan hajojin kasar Sin, ba zai warware gibin cinikayya da Amurka ke fuskanta ba.

Gao Feng ya ce karuwa ko raguwar gibin cinikayya, na da nasaba ne da yanayin kasuwa. Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin wani taron ganawa da 'yan jarida a jiya Alhamis, ya amsa wata tambaya dake da nasaba da batun karin harajin na Amurka.

Wasu alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta Sin sun nuna cewa, cikin watanni 8 kacal, ranar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya karu da kaso 7.7 bisa dari, adadin da ya tasarwa dalar Amurka biliyan 181, yayin da kuma yawan hajojin da ake shigarwa Amurka daga Sin suka karu da kaso 6.5 bisa dari.

A cewar Mr. Gao, karuwar yawan hajojin na da nasaba da karuwar bukatar su a kasuwannin Amurka, da ma karuwar sayayya daga manyan 'yan kasuwa, wadanda ke ganin mai yiwuwa karin harajin na Amurka, ya tsawwala farashin kayan da suke saya daga Sin.

Jami'in ya ce babban dalilin faruwar gibin cinikayyar Amurka, shi ne karancin kudaden ajiyar kasar, da matsayin dalar Amurka a jerin kudaden ajiyar kasa da kasa, da kuma tsoma hannun gwamnatin kasar a harkokin fitar da kayayyaki zuwa Sin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China