in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta zartas da dokar kasa ta al'ummar Yahudawa
2018-07-20 10:38:25 cri

A safiyar jiya 19 ga wata bisa agogon Isra'ila, majalisar dokokin Isra'ilar ta zartas da dokar kasa ta al'ummar Yahudawa, wadda ta yi tanadin cewa, al'ummar Yahudawa ita kadai ce ke da ikon gudanar da harkoki a cikin Isra'ila.

Wannan sabuwar doka ta yi tanadi a karon farko cewa, Isra'ila kasa ce ta al'ummar Yahudawa, kuma Yahudawa su kadai ne ke da ikon gudanar da harkokin cikin gidan kasar. Ban da wannan kuma, dokar ta bayyana birnin Kudus mai cike da 'yancin kai, a matsayin babban birnin Isra'ila, tare kuma mai da harshen Hebrew a matsayin harshen kasar, da kalandar Yahudawa a matsayin kalandar kasar.

Dadin dadawa kuwa, dokar ta yi tanadin cewa, kafa matsugunan Yahudawa, aiki ne da ya shafi moriyar kasar, saboda hakan, ya kamata kasar ta dauki mataki don aiwatar da wannan aiki yadda ya kamata.

Game da wannan doka, babban sakataren gudanarwa na kungiyar 'yantar da al'ummar Palasdinawa PLO Saeb Erekat, ya ba da wata sanarwa a wannan rana cewa, dokar ta halasta manufar wariyar kabilu daban daban, da kuma kwace iko na tsoffin mazaunan wurin. Kaza lika ma'aikatar harkokin waje ta Palasdinu ta ba da sanarwar cewa, dokar ta kasance wani mumunan mataki da ya sabawa doka, da yarjejeniyar kasa da kasa, ta kuma yi watsi da ka'idar jin kai. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China