A yayin ganawar, mista Zheng ya isar da gaisuwar shugaba Xi ga shugaba Keïta, ya kuma bayyana cewa, tun bayan kasashen biyu suka kulla huldar diplomasiyya a shekaru 58 da suka gabata, kullum suna nuna goyon baya ga juna, kasar Sin na fatan amfani da damar ta tabbatar da sakamakon da aka samu a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka da aka shirya a Beijing, don karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu a fannonin siyasa, tattalin arziki da tsaro da dai sauransu.
A nasa bangaren, shugaba Keïta ya nuna yabo sosai kan shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma manufar kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya kuma bayyana fatansa na ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Bilkisu)