in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manufar bude kofa da gyare-gyare a cikin gida na kushe da dimbin labarai da ya kamata duniya ta sani
2018-09-21 10:20:13 cri
Masu bada umarni da tsara shirye-shirye na musammam (Documentary), sun ce manufar kasar Sin, ta bude kofa ga kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a cikin gida, ta samar da dimbin abubuwa da duniya za ta yi sha'awarsu, kana akwai bukatar a yi bayaninsu yadda ya kamata.

Masu tsara shirye-shiryen sun bayyana haka ne a gefen wani taron kafafen watsa labarai da ya gudana domin karfafa gwiwar tsara shirye-shirye na musammam kan manufar bude kofa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin, wanda ofishin yada labarai na majlisar gudanarwar kasar Sin ya shirya.

A cewar Mathew Springford, babban mai tsara shiri a kafar yada labarai ta BBC, cikin sama da shekaru 40, sauyawar kasar Sin da ci gaban da ta samu cikin sauri na kunshe da abubuwa masu ban sha'awa.

Shi ma daraktan da ya taba samun lambar yabo ta Academy Malcom Clarke, wanda ya shirya shirin musammam na "Better Angels" na kasar Sin a shekarar 2016, ya ce akwai abubuwa bila-adadin da ya kamata a bayyana, domin duniya na bukatar fahimtar al'ummar Sinawa.

Yayin da take koyarwa a jami'ar Zhejiang, Hodan Osman Abdi, ta samu damar shirya wani shiri a bara, wanda ya kunshi rayuwar 'yan Afrika a birnin Yiwu na lardin Zhejiang, birnin da ya zama kasuwar kayakkin da ake samarwa a kasar Sin.

Ta ce dukkan 'yan Afrika 24 da suka fito a shirin, mutane ne kamar kowa kuma hadin gwiwa tsakanin Sinawa da 'yan Afrika masu tsara shirin, ya bada damar samun shiri mai inganci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China