Kwanan baya, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta dauki karin muhimman matakai, a fannonin fadada hanyoyin shiga kasuwanninta, da kara habaka shigar da kayayyaki da dai sauransu.
Game da hakan, kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Gao Feng, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka yi a yau cewa, a cikin shekaru 40 da suka gabata, tun fara gudanar da yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, kasar Sin ta cimma gagarumar nasara. Don haka, ana iya fahimtar cewa, muddin kasar Sin ta aiwatar da manufar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, za ta iya tabbatar da ci gabanta. Don haka, bisa son ranmu ne muke sanar da wadannan matakai na kara bude kofa ga kasashen waje, ta yadda kuma kasashen ketare za su amfana daga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.(Bilkisu)