Gwamnan babban bankin kasar Sin Yi Gang wanda ya sanar da hakan yayin taron manema labarai, ya ce dokokin hukumar da aka yiwa gyaran fuska za su baiwa masu sha'awar zuba jari na kasashen ketare damar mallakar kamfanoni kasuwar hannayen jari na hadin gwiwa, tare da alkawarin fadada hada-hadar irin wadannan kamfanoni.
Ya ce, an dauki wadannan matakai ne kamar yadda hukumomi suka sanar a dandalin shekara-shekara na Asiya na Boao da ya gudana a farkon wannan wata. (Ibrahim)