in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahaukaciyar guguwar Mangkhut ta isa yankin gabar tekun kudancin Sin
2018-09-16 19:58:27 cri
Tashar ba da bayanai game da hasashen yanayi ta lardin Guangdong na kasar Sin ta sanar da cewa, mahaukaciyar guguwar Mangkhut mai tafe da ruwa da iska mai karfi ta isa gabar birnin Jiangmen na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin da misalin karfe 5 na yammancin Lahadin agogon kasar Sin, kana saurin tafiyar guguwar ya kai kilomita 162 cikin sa'a guda.

Rahotanni na cewa, sama da mutane miliyan 2.45 ne aka kwashe daga gidajensu, baya ga kwale-kwalen kamun kifi sama da 48,000 da aka dawo da su tashar ruwan lardin da misalin karfe 5 na yammacin yau.

Yanzu haka an dakatar da ayyuka a sama da wuraren gine-gine 29,000 kana an rufe wuraren yawon shakatawa 632 dake yankin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China