A cewar cibiyar, da misalin karfe 5.00 na safe agogon kasar Sin an hango mahaukaciyar guguwar a tekun kudancin kasar Sin kimanin kilomita 420 daga kudu maso birnin Taishan na lardin Guangdong.
Cibiyar ta kara da cewa, yau Lahadi da kuma gobe Litinin yankunan kudancin kasar da suka hada da lardunan Guangdong da Fujian da Hainan, za su fuskanci ruwa da iska mai karfi.
Kasar Sin na da launukan matakan gargadi kan yanayi mai muni guda hudu, kuma launin ja, ya kasance mafi tsanani, sai launin ruwan goro da rawaya da kuma shudi.(Ibrahim)