in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron wakilan hadaddiyar kungiyar nakasassu ta Sin karo na 7
2018-09-14 21:06:20 cri
Yau Jumma'a da safe, aka bude taron wakilan hadaddiyar kungiyar nakasassu ta Sin karo na 7 a birnin Beijing, wanda ya samu halartar Shugaba Xi Jinping da sauran shugabannin kasar.

A jawabinsa yayin taron, mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng ya ce, sakamakon sabon ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin shekaru biyar da suka gabata, sha'anin nakasassu na kasar ya samu babban ci gaba. Kasar Sin ta bullo da matakan inganta jin dadin nakasassu da yawansu ya kai mutane fiye da miliyan goma, wanda ya hada da ba da kudin tallafi don inganta rayuwarsu, da ba da kulawa da ma warkar da yara. Sa'an nan an fito da wasu matakai bisa yanayin da ake ciki domin warware matsalar fama da talauci da nakasassu fiye da miliyan ke fuskanta.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China