Game da farashin amfanin gona na duniya a shekaru 10 masu zuwa. rahoton ya bayyana cewa, bukatun amfanin gona da hatsi a duniya zai ragu, kana hukumomin aikin noma za su ci gaba da inganta karfin samar da kayayyaki, don haka farashin amfanin gona a shekaru 10 masu zuwa ba zai karu ba.
Amma rahoton ya yi nuni da cewa, kasashe mafiya samun karuwar yawan mutane, musamman kasashen yankin gabas ta tsakiya, da arewacin nahiyar Afirka, da kudu da hamadar Sahara, da nahiyar Asiya, za su kara shigar da amfanin gona da hatsi cikin yankunansu. (Zainab)