in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaki da fatara shine babban jigon kare hakkin bil adam, inji jami'an diplomasiyya
2018-09-14 16:41:38 cri
Wasu manyan jami'an diplomasiyya na kasashen duniya daban daban sun jaddada muhimmancin rage fatara da kuma kyautata kare hakkin dan adam, a yayin taron kare hakkin dan adam na MDD karo na 39.

Sun bayyana ra'ayoyinsu ne a gefen taron MDD, wanda aka yiwa taken "Kawar da talauci da kyautata kare hakkin dan adam, bada kariya da kuma bayar da dukkan hakkokin bil adama, ciki har da hakkin cigaban dan adam."

Yu Jianhua, shugaban jakadancin Sin a ofishin MDD dake Geneva, yace kawar da talauci shine muradin farko na ajandar samar da dawwamamman cigaban duniya nan da shekarar 2030 kuma ya kasance muhimmiyar hanyar daga daraja da kare hakkin bil adama.

A cewar Yu, a cikin shekaru 5 kadai, sama da Sinawa miliyan 68 ne suka samu nasarar fita daga kangin fatara, wanda adadin shi ne kashi 70 bisa 100 na yawan wadanda suka yi ban kwana da talauci a duniya baki daya, hakan ya sanya kasar Sin ta kasance kasa ta farko da ta cimma nasarar cigaban muradun karni na yaki da fatara.

Nozipho Joyce Mxakato-Diseko, zaunannen wakilin kasar Afrika ta kudu a ofishin MDD dake Geneva yace, kamar yadda tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela ya fada, kawar da talauci ba alamu ne na bada jinkai kadai ba, "ya kasance a matsayin adalci ne, shi ne muhimmin jigon kare hakkin dan adam, da hakkin tabbatar da martabar dan adam da kuma baiwa dan adam hakkinsa na samar masa da ingantacciyar rayuwa."

Kimanin jami'an diplomasiyya 80 daga kasashen duniya sama da 30 da suka hada da Rasha, Jamus, Japan, Sweden, Singapore, Najeriya, Algeria, Venezuela da Argentina, da wasu wakilan hukumomin kasa da kasa ne suka halarci taron, wanda kasar Sin da hadin gwiwar Afrika ta kudu suka dauki nauyinsa. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China