in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta mayar da martani ala tilas kan matakin Amurka na kara karbar haraji
2018-09-06 18:53:07 cri
Kwanan baya kasar Amurka ta kawo karshen aikin sauraron ra'ayoyin jama'a game da shirinta na kara karbar haraji kan kayayyakin dake shigowa daga kasar Sin wadanda ke da darajar dalar Amurka biliyan 200. An ce, ko da yake sama da kashi 90 cikin dari na 'yan Amurka da suka bayyana ra'ayoyinsu na rashin amincewa da matakin, amma duk da haka gwamnatin kasar Amurka na fatan tsayawa kan inganta matakin.

Game da haka, kakakin ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin Gao Feng ya bayyana a taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis cewa, idan Amurka ta yi fatali da ra'ayin yawancin kamfanoni na nuna rashin amincewa, kuma ta tsaya kan daukar matakin kara karbar haraji kan kayayyakin kasar Sin, to kasar Sin za ta mayar da martani ala tilas.

Gao ya jadadda cewa, yakin cinikayya ba zai iya warware matsaloli ba, sai dai ta hanyar yin shawarwari na zaman daidai wa daida da sahihiyar zuciya kawai za a iya warware takaddamar ciniki a tsakanin Sin da Amurka. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China