in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron bada lambobin yabo ga masu aikin jin kai na kasar Sin karo na 10
2018-09-13 20:35:35 cri
A yau Alhamis 13 ga wata, an gudanar da taron bada lambobin yabo ga masu aikin ba da agaji na kasar Sin karo na 10 a nan birnin Beijing, inda aka bayar da lambobin yabo ga mutanen da suka yi fice a ayyukan ajin kai 28 da ayyukan jin kai 49 da kamfanoni 37 wadanda suka yi aikin ba da taimakon jin kai da kuma mutane 16 da suka bada gudummawar kudi. A jawabinsa yayin taron mataimakin ministan harkokin jama'a na kasar Sin Zhan Chengfu ya yi nuni da cewa, aikin da mutane ko kamfanoni suka yi don jin dadin jama'a ya shaida al'adun gargajiya na taimakawa juna na al'ummar kasar Sin, da yada aikin jin dadin jama'a, da samar da yanayi mai kyau a zamantakewar al'ummar kasar, da sa kaimi ga raya sha'anin yin aikin kula da jin dadin jama'a a kasar, da kuma bada jagoranci da zama abin misali a wannan fanni. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China