Rawar da kasar Sin ta taka ya fi na kowanne a nahiyar Asiya. Jami'ar Tsinghua ce ta zo na 9, inda Jami'ar Peking ta zo na 20 a cikin jerin jami'o'i 20 na farko.
Daliban da suka fi kwazo a kasar Sin su ne wadanda aka yaye daga jami'ar Peking. Kuma ita ce ta samu maki mafi yawa na alkaluman dalibai masu hazaka da ta yaye a kasar, kana ita ce mafi maki ta 25 a duniya.
Jami'o'i 3 na kasar Sin na daga cikin jami'o'i 20 da suka fi samun maki a fannin hadin gwiwa da masu daukar aiki, jami'o'in sun hada da Jami'ar Zhejiang wadda ta zo na 2 sai jami'ar Tsinghua a matsayi na 3 da kuma jami'ar kimiyya da fasaha ta Huazhong a matsayi na 19.
A bana, Jami'ar fasaha ta Massachusetts ce ta zo na daya a karon farko, inda ta ture Jami'ar Standford zuwa mataki na 2 a duniya. (Fa'iza Mustapha)