in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alcacer na kulob din Barcelona ya kulla yarjejeniya da Dortmund
2018-08-30 10:49:16 cri
Kungiyar wasan Borussia Dortmund ta sanya hannu don karbar hayar dan wasa mai tsaron baya Paco Alcacer daga kungiyar wasan FC Barcelona.

Dortmund ta gane muhimmancin dan wasan mai shekaru 24 a duniya inda suka nemi dan wasan da ya taka musu leda na tsawon shekaru 4.

"Muna matukar farin ciki yayin da Paco Alcacer ya bar kungiyar wasan Dortmund. Mun gamsu cewa wannan shine irin dan wasan da ya dace da tsarinmu. Paco ya tabbatar da ingancin da yake dashi ne a lokacin da matashin dan wasan ya taka leda ga kungiyar wasan Valencia kuma ya ci mata kwallaye masu yawa. A kungiyar Barcelona, yayi wasa tare da wasu daga cikin kwararrun yan wasa na duniya," daraktan wasan Dortmund Michael Zorc ne ya bayyana hakan.

Alcacer ya buga wasa tun a kakar wasanni ta 2016 ga Barcelona kuma ya bayyana a wasanni 51, inda ya zura kwallaye 15, kana ya bada taimako wajen cin kwallaye 8.

"Hakika ina matukar son taka leda a Bundesliga nan gaba kadan. Wannan shine wasanni mafi kyau a duniya kuma wasannin na BVB dake da irin wadannan magoya baya da ba'a taba tsammani ba da katafaren filin wasa yana da wani abu na ban mamaki dake bayyanwa 'yan wasan kwallon kafa," inji Spaniard.

Borussia Dortmund zasu fafata da Hannover domin fara zagaye na biyu na wasannin Bundesliga a ranar Juma'a.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China