in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AEK Athens ta samu gurbi a gasar UEFA
2018-08-30 10:47:23 cri
Bayan kwashe shekaru 12 tana yunkurin samun wannan dama, kungiyar AEK Athens ta samu gurbi na buga gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA Champions League ajin rukunoni. Kungiyar ta samu wannan dama ce bayan da ta yi kunnen doki 1 da 1 da kungiyar MOL Vidi ta kasar Hungary a filin wasa na Athens OAKA. Sakamakon wasan ya sanya AEK Athens shigewa gaban MOL vidi da yawan kwallaye 3 da 2 a wasannin da suka buga gida da waje.

Kyaftin din kungiyar Petros Mantalos ne ya ciwa AEK Athens kwallo a wasan ranar Talata cikin minti na 47, ta bugun da ga kai sai mai tsaron gida. Kafin daga bisani Loic Nego ya farkewa kungiyar Vidi kwallon ta bayan mintuna 10 kacal.

Ana ruwan sama kamar da bakin kwarya, AEK Athens ta rike wasan har tashi, duk kuwa da jan kati da aka baiwa dan wasan ta Helder Lopes a minti na 80th da take wasa.

Yanzu haka dai kungiyar ta kasar Girka na jiran a ware rukunonin gasar a Alhamis din nan a birnin Monaco, domin sanin kungiyoyin da za ta fafata da su a rukuni guda na gasar ta UEFA Champions League.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China