in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaunannen wakilin Sin a WTO ya bada sanarwa kan takardar da Amurka ta fitar
2018-04-04 10:37:55 cri
A safiyar yau Laraba, zaunannen wakilin Sin dake hukumar ciniki ta kasa da kasa wato WTO, Zhang Xiangchen, ya bada sanarwa don maida martani ga takarda mai lamba 301 ta dokar ciniki ta kasar Amurka wanda ta kunshi matakan da Amurkar zata dauka kan kasar Sin a fannin cikini. Sanarwar ta nuna cewa, rahoton da aka bayar cikin wannan takarda babu kamshin gaskiya cikinsa, kuma zargin da aka yi wa kasar Sin ba daidai ba ne, sa'an nan abubuwan da rahoton ya fadi ya ci karo da hakikanin halin da Sin take ciki na sa kaimi ga yin kwaskwarima kan kasuwar Sin da kara bude kofa ga kasashen waje da kara kare ikon mallakar ilmi.

Sanarwar ta ce, bisa rahoton da Amurka ta bayar mai lamba 301, na kara dorawa kayayyaki kirar kasar Sin haraji da taka mata birki a fannin zuba jari ya sabawa ka'idojin hukumar ta WTO, inda ta baiwa wasu kasashe fifiko na musamman da kayyade haraji ga sauran kasashe, wanda ya kasance mataki ne na kashin kanta kawai da kuma manufar kariyar ciniki. Sin ta kuma kalubalanci batun da kakausar murya. Ban da wannan kuma, sanarwa ta ce, Sin zata dauki matakan da suka dace don kare moriyarta. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China