in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon Sin: Afirka muhimmiyar kawace a shawarar ziri daya da hanya daya
2018-06-14 10:10:11 cri

Wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, nahiyar Afirka muhimmiyar kawace a ci gaban shawarar ziri daya da hanya daya. Manzon na Sin wanda ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani na manyan jami'ai da aka shirya game da shawarar a hedkwatar MDD, ya ce manufar shawarar ita ce biyan bukatun nahiyar da samun moriyar juna ba tare da gindaya wani sharadi na siyasa ba.

Bugu da kari, shawarar, za ta taimakawa nahiyar Afirka ta hanyar mutunta juna da fadada abokanta da amfana da wasu damammaki ta hanyar ba da fifiko ga abokantakan dake tsakani.

Sama da kasashen nahiyar Afirka 20 ne dai suka shiga shawarar ta ziri daya da hanya daya, wadanda suka hada da Masar da Kenya, Uganda, da Najeriya da Kamaru da kasar Afirka ta kudu. Haka kuma an cimma yarjejeniyar hadin gwiwa kan muhimman ayyuka 39 wadanda suka shafi fannoni 17 kamar gina hanyoyin jiragen kasa da tagwayen hanyoyin mota da tashoshin jiragen ruwa da samar da hasken wutar lantarki.

An kuma gina sabbin kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afirka, wadanda suka hada da rukunin masana'antu, layukan dogo, hanyoyin mota, da filayen jiragen sama da tashoshin samar da wutar lanyarki, matakin da ya kara bunkasa nahiyar.

A shekarar 2017 ne bisa taimakon kamfanoni da gwamnatin kasar Sin, rukunin masana'antu na farko na Hawassa dake kasar Habasha ya fara aiki, inda ya samar guraben ayyukan yi 60,000 baya ga kudaden shigar da suka kai dala biliyan 1 da kasar Habashan take samu a ko wace shekara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China