in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon jirgin sama mallakar Nijeriya zai samu izinin fara aiki
2018-09-05 09:18:36 cri

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya, ta ce za ta ba da lasisin sufuri da shaidar izinin gudanar da aiki ga sabon jirgin saman Nijeriya cikin kwanaki 90 masu zuwa.

Darakta janar na hukumar Muktar Usman, ya ce har yanzu akwai yiwuwar jirgin ya fara aiki a watan Disamban bana kamar yadda aka tsara.

Lasisin sufuri da za a ba jirgin shi ne matakin karshe na ba shi izinin fara gudanar da aiki, wanda kuma hukumar kula da sufurin jiragen sama ce ke da alhakin badawa, domin ba shi damar fara zirga-zirga da daukar fasinjoji.

Usman Muktar, ya kuma tabbatarwa al'ummar kasar cewa, gwamnati na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da nasarar fara aikin jirgin.

A ranar 18 ga watan Yuli ne gwamnatin Nijeriya ta bayyana suna da tambarin sabon jirgin a wajen taron baje kolin jiragen sama na Farnborough Air Show a birnin London. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China