in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Birtaniya sun sanya hannu kan yarjejeniyar tattalin arziki da tsaro
2018-08-30 09:29:55 cri

A jiya Laraba kasashen Najeriya da Birtaniya sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi biyu da suka shafi tattalin arziki da tsaro, matakin ya biyo bayan wata ganawar sirri da ta gudana ne tsakanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da firaiministar Birtaniya Theresa May a Abuja, wacce ke ziyara a Najeriya.

May ta ce, ziyararta ta shafi batun kyautata alakar tattalin arziki ne da Najeriya, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin shugaban Najeriyar ta tabbatar da hakan.

"A tare da ni akwai tawagar wakilan 'yan kasuwa, a yayin da muke kokarin karfafa dangantakarmu a nan gaba da kuma lalibo karin damammakin cinikayya," in ji firaiministar ta Birtaniya.

May ta ce, Birtaniya za ta kara hada gwiwa da Najeriya wajen kawar da muggan laifuka, da yaki da safarar bil adama da kuma yaki da rashawa.

Buhari ya yi alkawarin cewa, Najeriya a shirye take ta karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu, ya ce, Najeriya tana kokarin kara kyautata alakarta da Birtaniya wajen magance rashawa da rage radadin talauci.

Firaiministar za kuma ta ziyarci birnin Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya, daga bisani ta zarce zuwa kasar Kenya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China