in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama wani mutum da ya yi kokarin kai hari a kusa da ofishin jakadancin Amurka dake Alkahira
2018-09-05 10:37:36 cri

Ma'aikatar watsa labarai ta kasar Masar ta sanar da cewa, an kama wani matashi dan shekara 24 mai suna Abdullah Ayman Abdel-Samea a jiya Talata, lokacin da wata kwalba mai dauke da sinadarai dake cikin jakar dake bayansa ta kama da wuta a kusa da ofishin jakadancin Amurka dake birnin Alkahiran Masar.

Sanarwar ta ruwaito kafofin tsaro na cewa, mutumin mai tsattsauran ra'ayi, ya yi niyyar kai hari da kwalbar ce. Lamarin ya faru ne a titin Simon Bolivar kusa da ofishin jakadancin kasar ta Amurka mai cike da matakan tsaro dake tsakiyar birnin Alkahira. Sai dai sanarwar ta ce ba a samu rahoton jikkata ko wata barna ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China