in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya lashe zaben shugaban kasar a wa'adi na biyu da kaso 97.08 na kuri'un da aka kada
2018-04-03 09:27:58 cri

Shugaban Masar mai ci Abdel-Fattah al-Sisi, ya lashe zaben shugaban kasar da gagarumin rinjaye, inda ya samu kaso 97.08 bisa dari na kuri'un da aka kada.

A ranar 19 ga watan Maris ne aka kammala zabe na 'yan asalin kasar dake kasashe 124 na fadin duniya, yayin da zabe a cikin kasar ya gudana a ranekun 26 da 28 na watan na Maris.

An gudanar da zaben ne karkashin tsauraran matakan tsaro a cibiyoyin zaben dake fadin kasar.

Shugaba Al-Sisi ya kama aiki ne a shekarar 2014, shekara guda bayan ya jagoranci hambarar da tsohon shugaba Mohammed Morsi a matsayinsa na babban kwamandan soji, a wani martani ga zanga-zangar da al'ummar kasar suka yi na nuna adawa da gwamnatin Morsi da kungiyarsa ta 'yan uwa musulmi.

Galibin 'yan kasar da suka zabi Sisi sun yi ammana da shi a matsayin wanda ya ceto kasar daga hannun kungiyar masu tsatsauran ra'ayi da a yanzu aka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda, sannan sun amince karkashin shugabancinsa, za a kawar da ta'addanci tare da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali da kuma ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China