in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar tana sa ran za a cimma matsaya game da batun madatsar ruwa ta Habasha
2017-12-26 10:07:29 cri

Ministan noman rani na kasar Masar Mohamed Abdel-Aati, ya bayyana burin kasarsa na cimma matsaya kan madatsar ruwa ta Ethiopian Grand Renaissance Dam wato (GERD).

Kamfanin dillancin labaran kasar MENA ya rawaito Abdel-Aati yana bayyana wa 'yan majalisun dokokin kasar cewa, kasar Masar ba za ta shiga duk wata yarjejeniyar da za ta kawo illa ga batun kiyaye harkokin ruwanta ba.

Ministan ya sanar da cewa, ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry, zai ziyarci kasar Habasha cikin wannan mako, gabanin ziyarar da takwaransa na kasar Sudan zai kai kasar ta Masar din a makon gobe a matsayin daya daga cikin yunkurin cimma matsaya game da madatsar ruwan ta Habasha.

Masar ta nuna damuwa game da adadin ruwa cubic mita biliyan 55.5 da suke rabawa juna a shekara na kogin Nile, a daidai lokacin da take tsaka da aikin gina madatsar ruwan ta GERD.

Dangantakar dake tsakanin Masar da Habasha ta fara yin tangal-tangal ne tun daga lokacin da ta fara aikin gina madatsar ruwan a watan Afrilun shekarar 2011, a lokacin ne kuma kasar ta Masar ta fada cikin tashin hankali sakamakon hambarar da gwamnatin shugaba Husni Mubarak na kasar.

A lokacin da Abdel-Fattah al-Sisi ya karbi mulkin kasar a shekarar 2014, ya nuna sha'awarsa ta ci gaba da aikin gina madatsar ruwan ta GERD wanda ake sa ran zai samar da karfin hasken lantarki megawatts 6,000.

A watan Maris na shekarar 2015, shugabannin kasashen Masar, Habasha da Sudan, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar farko ta yin amfani da kogin Nile da kuma gina madatsar ruwan ta GERD, wanda zai kasance madatsar ruwa mafi girma a nahiyar Afrika idan aikin ya kammala.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China