in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaminista: Habasha ba za ta kawo illa ga kason ruwan da Masar take samu daga kogin Nilu ba
2018-06-11 13:09:06 cri

Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali ya lashi takwabin cewa, aikin gina babbar madatsar ruwan da kasarsa take yi ba zai kawo nakasu ga kason ruwan da kasar Masar take samu daga kogin Nilu ba.

Firaministan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron manema labarai na hadin gwiwa da suka shirya tare da shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar a birnin Alkahira, biyo bayan tattaunawarsu kan aikin gina babbar madatsar ruwa da ya ratsa kogin na Nilu.

Ya ce, ya rantse da Allah, Habasha ba za ta kawo illa da ruwan da Masar din take samu daga kogin Nilu ba.

Wannan dai ita ce ziyarar firaministan na Habasha ta farko a kasar Masar tun lokacin da ya kama aiki a watan Afrilu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China