in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin sarrafa magungunan Sin na fatan shiga kasuwannin Najeriya
2018-08-29 10:01:58 cri

Wasu wakilai na kamfanonin harhada magunguna na kasar Sin sun isa Najeriya, domin duba yiwuwar yin hadin gwiwa da abokan hulda na kasar.

Rahotanni na cewa, tawagar na karkashin jagorancin babban sakataren cibiyar kasuwancin kasar Sin fannin hada hadar kayayyakin kiwon lafiya da magunguna Mr. Tan Shengcai. Tuni kuma wakilan suka halarci wani taron masu ruwa da tsaki jiya Talata a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, domin tattaunawa game da yanayi, da irin ribar dake tattare da kasuwar magungunan kasar.

Da yake tsokaci game da dalilin zuwan su Najeriya, Mr. Tan ya shaidawa taron masu zuba jari da kasuwancin kayayyakin kiwon lafiya a Lagos din cewa, suna fatan haduwa da abokan hulda a Najeriya, domin gudanar da hadin gwiwar kasuwanci mai dorewa.

A na ta tsokaci, babbar darakta a hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, uwargida Moji Adeyeye, ta bayyanawa mahalarta taron irin kokari da Sin ke yi, wajen tallafawa Najeriya a fanni raya masana'antun ta. Ta kuma ja hankulan kamfanonin harhada magunguna na Sin, da su yi hadin gwiwa da takwarorin su na Najeriya a fannin gudanar da bincike, da samar da ci gaba mai ma'ana.

Kafin hakan a ranar Litinin, tawagar ta 'yan kasuwar Sin ta ziyarci yankin ciniki cikin 'yanci na Lekki dake gabashin birnin na Lagos, wanda aka kafa sakamakon hadin gwiwar masana'antun Sin da na Najeriya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China