in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyya mai mulkin Nijeriya ta zargi hukumar zaben kasar da kwarmata wasu bayananta
2018-08-25 15:52:23 cri

Jam'iyya mai mulkin Nijeriya APC, ta zargi hukumar zaben kasar, da kwarmata bayanan babban taronta da na zaben fidda gwani da ta mika mata.

Sanarwar da kakakin jam'iyyar APC Yekini Nabena ya fitar, ta ce akwai bukatar hukumar zaben ta duba yadda ake kula da bayanan sirri domin kawo karshen irin wannan kwarmatar.

Kakakin ya ce, jam'iyyar na sane da kwarmata wata wasika da shugabanta na kasa Adams Oshiomhole ya aike wa hukumar, inda yake sanar da ita game da lokutan da jam'iyyar ta shirya gudanar da babban taronta da kuma zaben fidda gwanin masu son tsayawa takara a zaben 2019. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China