in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#FOCAC#Sin za ta kafa asusun kiyaye zaman lafiya a Afirka
2018-09-03 17:48:53 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa ta tsai da kuduri cewa, za ta kafa asusun kiyaye tsaro a kasashen Afirka domin ba da goyonta ga hadin gwiwar kiyaye zaman lafiya dake tsakaninsu, kana za ta ci gaba da samar da tallafin aikin soji ga AU ba tare da gindaya wani sharadi ba, ta yadda kungiyar za ta cimma burinta na kiyaye zaman lafiya da yaki da ta'addanci a yankin Sahel da tekun Aden da tekun Guinea da sauran yankunan nahiyar. Kana za ta kafa wani dandali, inda sassan biyu wato Sin da Afirka za su rika tattauna harkokin tsaro a tsakaninsu, ta yadda za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare kuma da gudanar da ayyukan tallafi kan fannoni tsaro guda 50 kamar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da kiyaye kwanciyar hankali, da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, da dakile barazanar 'yan fashin teku, da yaki da ta'addanci da sauransu lami lafiya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China