Yau Litinin a yayin taron kolin dandalin FOCAC da ake gudanarwa a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa ta tsai da kuduri cewa, za ta fara aiwatar da "shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka kan aikin gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a" ta hanyar hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Afirka AU, kuma za ta goyi bayan kamfanoninta domin su shiga ayyukan zuba jari da shiga aikin ginawa da kuma tafiyar da wadannan harkoki a kasashen Afirka, musamman ma ayyukan da suka shafi makamashi da sufuri da sadarwa da samar da albarkatun ruwa da sauransu, ta yadda sassan biyu wato Sin da Afirka za su samu moryar juna.(Jamila)