Kamata ya yi, Sin da kasashen Afirka su karfafa tattaunawar siyasa da cudanyar manufofi a matsayi daban daban, da kara hada kai a sabbin fannoni, da raya sabbin fannoni na tattalin arziki, kana da samar da hakikanin nasarori ga jama'ar bangarorin biyu, da kuma kara yin mu'amala a fannonin al'adu, fasaha, ba da ilmi, da wasannin motsa jiki da dai sauransu. Baya ga haka, ya kamata a tsaya tsayin daka kan goyon bayan kasashen Afirka da wasu kungiyoyin shiyyar, ciki har da AU, don su warware matsalolinsu bisa hanyar da ta dace da su, haka akwai bukatar bangarorin biyu su karfafa hadin kai a fannin sauyin yanayi da sauran fannoni da suka shafi kiyaye muhalli. (Bilkisu)