in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#FOCAC#Sin ta hakkake zaman lafiya da ci gaba suna abu mafi muhimmanci ga daukacin kasashen duniya
2018-09-03 17:17:52 cri

Yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta hakkake cewa, zaman lafiya da samun ci gaba suna abu mafi muhimmanci ga ko wace kasa a fadin duniya, a sabon zamanin da ake ciki, kasar Sin ta sauke nauyin ciyar da sha'anin bil Adama gaba a wuyanta, kana tana son hada kai tare da sauran kasashen duniya karkashin laimar shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda za a gudanar da harkokin kasashen duniya yadda ya kamata.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufofin bude kofa ga ketare, da kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, da tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori da dama, haka kuma tana adawa da manufar duk wata ta ba da kariya ga harkar cinikayya, da tsarin gudanar da cinikayya bisa bangare guda, saboda hakan zai kawo illa ga makomar kasa kanta.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China