#FOCAC#Xi Jinping ya ce sam kasar Sin ba za ta yi abun da bai dace ba yayin hadin-gwiwarta da kasashen Afirka
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Litinin ya bayyana cewa, hadin-gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, hadin-gwiwa ce mai salon musamman kana ta samun moriyar juna. Ya ce yayin da kasar Sin ke kokarin karfafa hadin-gwiwa da kasashen Afirka, sam ba za ta yi abubuwan da ba su dace ba, yana mai cewa ba za ta tsoma baki kan yadda kasashen Afirka ke kokarin neman samun bunkasuwa ba, kuma, ba za ta yi shiga sharo ba shanu cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka ba, kana, ba za ta tilastawa kasashen Afirka amincewa da dukkanin ra'ayoyinta ba, kana kuma, ba za ta gindaya wani sharadin siyasa kan kasashen ba a yayin da take samar masu da tallafi, haka zalika, kasar Sin ba za ta nemi samun moriya ita kadai ba, yayin da take kokarin zuba jari a kasashen Afirka.(Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku