in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka su shigo a gina shawarar "Ziri daya da hanya daya"
2018-09-03 16:31:59 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce kasarsa na goyon bayan kasashen Afirka su shiga a dama da su wajen gina shawarar "ziri daya da hanya daya" ta yadda sassan biyu za su amfana da sakamakon da zai biyo baya.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a yau Litinin yayin da yake yiwa taron shugabanni da wakilan 'yan kasuwan Sin da Afirka jawabi.

Ya ce, a shirye kasar Sin take ta karfafa alakarta da kasashen Afirka ta yadda za a gina hanyar ci gaba mai inganci da ta dace da yanayin kasashen, ta yadda kowa ne bangare zai ci moriya.

Jawabin shugaban mai take "aiki tare don samun kyakkyawar makoma" shi ne kuma taron 'yan kasuwar Sin da Afirka karo na shida.

Shugaba Xi ya ce, kokarin samar da kyakkyawar makoma ga dukkan al'ummomin kasashen duniya, ciki har da al'ummar Afirka wani muhimmin bangare ne na gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil-Adama.

Ya kara da cewa, kasar Sin ba ta gindaya wani sharadi na siyasa yayin da take zuba jari a Afirka karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, haka kuma ba ta shiga harkokin cikin gidan kasashen Afirka ko tilasta musu bukatunta.

Shugaba Xi ya ce alakar Sin da Afirka karkashin shawarar, tana mayar da hankali wajen samar da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da sauran muhimman sassan dake hana ci gaban Afirka, za ku a yi amfani da kudade a wuraren da ake matukar bukatan hakan.

Ya ce, kasashen Sin da Afirka na kokarin raya shawarar ziri daya da hanya daya kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. Yana mai cewa, a shirye kasar Sin take ta karfafa alaka da duk wata kasa dake da iko da kuma muradun yin haka.

Shugaban ya ce, kasarsa na maraba da 'yan kasuwa daga ko'ina a duniya, ciki har da kasashen Afirka, don su zuba jari da raya kasar Sin, tana kuma karfafawa kamfanonin kasar Sin gwiwar da su gudanar da harkokin kasuwanci a Afirka, ta yadda za su raya shawarar ziri daya da hanya daya tare. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China