Shugabanni ko wakilai na kasashen Afirka 53, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka AU Moussa Faki Mahamat, da masu sa ido da suka fito daga kungiyoyin kasa da lasa da na shiyya shiyya guda 27 ne suka halarci taron. A yayin taron da taken "Hada kai da samun nasara tare, da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan al'umomin Sin da Afirka", za a tsara shirye-shirye kan wasu muhimman fannonin da bangarorin biyu za su karfafa hadin kai nan da shekaru 3 masu zuwa, da ma nan gaba. (Bilkisu)