Rahoton ya yi nuni da cewa, asusun IMF ya daga hasashen bunkasuwar tattalin arzikin duniya na shekaru masu zuwa ne, domin ya yi la'akari da bunkasuwar kasashe masu ci gaban tattalin arziki, da kuma kwaskwarimar tsarin haraji na kasar Amurka, da shirye-shiryen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar wadanda za su bunkasa tattalin arzikin kasar Amurka a wannan lokaci.
To sai dai kuma rahoton bai canja zaton bunkasuwar tattalin arzikin sabbin kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki da na kasashe masu tasowa ba.
Shugaban ofishin nazari na asusun IMF Maury Obstfeld ya yi nuni a gun taron manema labaru cewa, ko da yake an sassauta saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin, amma Sin ta kiyaye kasancewa kasar da ta fi sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Zainab)