in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na samar da agajin gaggawa domin taimakawa 'yan ci rani a Libya
2017-10-20 10:21:23 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya da ba da taimako ta MDD a Libya, ta ce hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD na samar da agajin gaggawa domin taimakawa 'yan ci rani a kasar Libya.

Tawagar ta ce, bayan shafe makonni ana kwabza fada a birnin Sabratha, a kalla 'yan ci rani 14,000 da a baya ake tsare da su a wasu cibiyoyi da sansanoni ne aka mai da wani matsuguni dake yankin Dahman na birnin, inda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ke ba su agajin gaggawa.

Hukumar na samar da abinci da ruwan sha da kayayyakin jin kai da suka hada da katifu da barguna da filallika da kayayyakin tsafta ga 'yan ci rani 2,600 wadanda su ne kashin farko da aka ajiye a wurin.

Sabili da yanayin rikici da rashin tsaro da suka biyo bayan rikicin shekarar 2011 a kasar, dubban 'yan ci rani ne suka zabi ratsawa Libya, su tsallake tekun Madateriniyan domin zuwa Turai.

Wadanda sojojin ruwan Libya suka ceto daga tekun ne aka tsarewa a wasu cibiyoyi da ba su da kyan yanayin zama.

Hukumar ta ce, za a ba wadanda ke son komawa kasashensu damar komawa karkashin shirinta na taimakawa masu bukatar komawa gida. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China