in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD na shirin sake bude karamin ofishinsa dake kudancin Libya
2017-10-26 09:45:24 cri

Wakilin musamman na babban sakataren MDD kana shugaban tawagar MDD a kasar Libya, Ghassan Salame ya ce yana fatan sake bude karamin ofishin majalisar dake garin Sebha na kudancin kasar Libya, a wani mataki na sanin irin wainar da ake toyawa a yankin, tun bayan rufe ofishin a shekarar 2013.

Salame ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da wakilan yankin kudancin kasar Libya jiya Laraba a birnin Tripoli, inda ya saurari bukatu da kalubalen da yankin kudancin Libyan yake fuskanta.

Salame ya ce, sake bude ofishin MDD a birnin na Sebha, zai baiwa MDDr damar kara yawan shirye-shiryenta na tallafi da take fatan aiwatarwa a yankunan kudancin kasar.

A jawabinsa, wakilin yankin kudancin kasar Libya a majalisar dokokin kasar, Ismail Sharif, ya ce al'ummar yankin sun zaku su shiga a dama da su cikin harkokin raya kasa tun lokacin da kasar ta fada cikin tashin hankali.

Kasar Libya dai ta shafe shekaru da dama tana fama da karancin ayyukan hidima da matsalar tsaro musamman rikicin kabilanci, da hare-haren da mayaka masu alaka da IS da suka kaura zuwa yankunan hadama da tsaunukan kudancin kasar suke kaddamarwa tun bayan da aka kwace garuruwan Benghazi da Sirte daga hannunsu. Haka kuma yankin ya yi fama da matsalar fashi da makamai, da sace mutane da safarar miyagun kwayoyi da na makamai.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China