in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce an kashe fararen hula 47 a Libya a Mayu
2018-06-02 15:09:31 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake aiki a Libya ta ce, rikici a kasar ya yi sanadin mutuwar fararen hula 47, tare da jikkata wasu 54 a watan Mayu.

Rahoton da tawagar ta fitar ya ce, a bayanan da take tattarawa, fararen hula 101 ne rikici ya rutsa da su, ciki har da harin bam na cikin mota da hare-haren kunar bakin wake a fadin Libya cikin watan Mayu, inda ya ce, adadin shi ne mafi yawa da aka samu a bana.

Ya kara da cewa, hare-haren nakiyoyi da bama-bamai da wasu ababen fashewa da ba a gano irinsu ba, da hari ta sama da harbe-harbe ne muhimman musababbin jikkatar fararen hular.

Cikin rahoton, tawagar ta bukaci dukkan bangarori a Libya, su tsagaita kai hare-hare a yankunan dake da yawan fararen hula, sannan kada su girke makaman yaki a wuraren da ke da cikowar jama'a.

Har ila yau, rahoton ya bukaci a dakatar da kisan gillar da ake wa wadanda aka kama, kuma dole ne a rika tafiyar da su, ciki har da mayakan da aka kama, yadda ya kamata a kowanne hali. Haka zalika, ya ce, gallazawa da kisan wadanda aka kama laifi ne na yaki, ba tare da la'akari da abun da wanda ake zargin da aikatawa ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China