in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kroos ya zama zakaran kwallon kafar Jamus na bana
2018-08-09 15:19:58 cri

Dan kwallon tsakiya na kasar Jamus Toni Kroos, ya zama zakaran kwallon kafar kasar na bana, kamar yadda mujallar kicker Sports ta bayyana.

Dan kwallon mai shekaru 28 da haihuwa, ya kai ga nasarar karramawar ne ta bana wadda ita ce ta 59, bayan da aka kada kuri'un amincewa da kwarewar sa.

'Yan jaridu dake bibiyar kwallon kafa su 475 ne suka kada kuri'un su a wannan karo, inda 185 suka jefawa Kroos kuri'a. A bara mai dai Kroos din ne ya kasance a matsayi na biyu, a jerin 'yan wasan kasar ta Jamus mafiya kwarewa.

Baya ga Kroos, sauran 'yan wasan da ke tashe sun hada da dan wasan gaban kulaf din Freiburg Nils Petersen, wanda ya kasance a matsayi na biyu da kuri'u 39, sai kuma dan wasan bayan Schalke Naldo a matsayi na 3 da kuri'u 38.

A daya bangaren kuma, an zabi tsohon kocin Kroos Jupp Heynckes da kuri'u 91, a matsayin koci mafi kwarewa a kasar ta Jamus. Sai kocin Schalke Domenico Tedesco a matsayi na biyu da kuri'u 89. Yayin da kocin Bayern Munich Robert Kovac ya zamo na 3 da kuri'u 77.

Da yake tsokaci bayan zaben na sa, Jupp Heynckes ya ce, ya yi farin ciki matuka da kasancewar sa na daya, tsakanin dukkanin masu hosar da 'yan wasan Jamus a bana. Ya ce ya kuma godewa wadanda ma basu zabe shi ba, kasancewar ya yi imanin akwai masu hosar da 'yan wasan matasa da dama, dake da hazaka a kulaflikan dake buga gasar Bundesliga ta Jamus, wadanda su ma suka cancanci a karrama su.

A bangaren mata kuwa, 'yar wasan kwallon kafa Dzenifer Marozsan, ta sake lashe kuri'un kwarzuwar 'yar wasa ta bana, bayan da ta lashe wannan matsayi a bare. 'Yar wasan mai shekaru 26 da haihuwa, ta samu kuri'u 105, yayin da mai biye mata a matsayi na biyu ta Wolfsburg Pernille Harder ta samu kuri'u 70.

Gomez ya yi ritaya daga kungiyar kwallon kafar Jamus

Dan wasan gaban kasar Jamus Mario Gomez, ya bayyana kawo karshen bugawa kasar kwallo. Hakan ya biyo bayan rashin nasara da kasar ta fuskanta a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Rasha.

Da yake tsokaci game da yadda kwallo ta kasance masa a kungiyar, Gomez ya ce, zaman sa a kungiyar Jamus ba abu ne mai sauki ba, amma duk da kalubalen da ya fuskanta, a hannu guda ya ji dadin taka leda a kungiyar. Ya ce ya hadu da mutane da ko a nan gaba, za su cigaba da zumunci tsakanin su.

Dan wasan mai shekaru 33 da haihuwa, ya fara kwallo tun daga kungiyar matasan kungiyar, kafin daga bisani ya samu gurbi a babbar kungiyar kasar a watan Fabarairun shekarar 2007. Yayin da yake taka kwallo a kungiyar kasar ta Jamus, ya samu nasarar zura kwallaye 31 a wasanni 78 da ya buga.

Cikin sanarwar da ya fitar a karshen makon jiya, Gomez ya ce lokaci yayi da zai baiwa matasa masu jini a jika dama su ma su nuna tasu kwarewar.

Gomez ya kasance cikin tawagar Jamus a shekarar 2008, lokacin da suka zamo na biyu a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai. Da kuma a shekarar 2010, lokacin da Jamus din ta yi na uku a gasar cin kofin duniya na hukumar FIFA, wanda aka buga a kasar Afirka ta kudu.

Daga wannan lokaci kuma, Gomez zai mayar da hankali ga buga kwallo a kungiyar sa ta Stuttgart dake taka leda a gasar kalubalen kasar ta Jamus wato Bundesliga. A kakar wasa da za a bude, Stuttgart za ta fara wasan farko da Mainz a ranar 26 ga watan nan na Agusta.

Bayern Munich ta doke Manchester United da ci daya mai ban haushi

Javi Martinez na kungiyar kwallon kafar Bayern Munich, ya daga ragar Manchester United a wasan sada zumunta da suka buga a Lahadin karshen kamo, inda kulaflikan biyu suka tashi wasan da ci daya da nema.

Bayern Munich ce dai ta mamaye wasan baki daya, wanda masharhanta ke ganin Manchester United ba ta nuna wata bajimta a cikin sa ba.

'Yan wasan Bayern Munich karkashin koci Robert Kovac, sun yi wasa yadda ya kamata, yayin da 'yan wasan Manchester United karkashin koci Jose Mourinho suka yi ta yawo a fili, musamman a mintuna 45 na farkon wasan, yayin da ya rage 'yan kwanaki su fara taka leda a kakar wasan firimiyar Ingila da za a fara nan da 'yan kwanaki.

Sai da aka kai minti na 60 ana wasa, kafin Javi Martinez ya jefa kwallo daya tilo da aka ci a wasan a ragar Manchester United, ta bugun kwana wadda Thiago Alcantara ya dauko.

Da yake tsokaci game da yadda wasan ya gudana, koci Kovac ya yabawa 'yan wasan sa, bisa abun da ya kira kwazo da suka nuna. Ya ce "mun yi atisaye sosai a baya bayan nan. Wasan yau wanda muka mamaye ya nuna himmar mu maras iyaka," a kalaman kocin Bayern Munich Kovac. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China