Ana dai ganin hakan zai samarwa kungiyar ta Madrid damar daukar dan wasan gaba bayan da Cristiano Ronaldo ya yi sauyin sheka daga Madrid din zuwa Juventus a cikin watan Yulin da ya gabata.
Real Madrid ta sayarwa Lyon Mariano ne kan kudi har Euro miliyan 8 a kakar shekarar 2017, bayan da ya taka leda a ajin B na kungiyar ta Real. Yayin da yake taka leda, dan wasan ya ci kwallaye 21 a gasar wasannin kasar Faransa, matakin da ya sanya Sevilla nuna sha'awar ta ga sayen sa kan Euro miliyan 35. Bayan hakan ne kuma Real Madrid ta mika bukatar sake sayen sa kan Euro miliyan 22.
Game da hakan, shugaban kungiyar Sevilla Jose Castro, ya shaidawa 'yan jarida cewa, Madrid ba ta bayyana aniyarta ta sayen Marian ba,, sai da Sevilla ta nuna sha'awar sayen dan wasan. Amma duk da hakan Mr. Castro ya ce babu damuwa, haka kwallo ta gada, ba kuma za su yi fushi da hakan ba.(Saminu Alhassan)