"Na ayyana sunan babbar tawagar 'yan wasan wanda na yi imanin zasu wakilci kasarmu kuma zasu tsallake gasar share fagen cin kofin kwararru na AFCON," inji shugaban kungiyar wasan Uganda Peter Onen a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Wasan zai samu halartar kungiyoyin wasanni 10 daga majalisar wasannin kwallon kafa ta gabashi da tsakiyar Afrika wato (CECAFA), kuma za'a fara wasan ne a ranar 11 ga watan Augasta a Dar es Salaam, na kasar Tanzania. Uganda tana rukuni daya da Habasha, Djibouti, Sudan ta kudu da kuma Kenya a rukunin Pool B. Uganda zata fara wasanta na farko ne da Habasha a ranar 12 ga watan Augasta sannan daga bisani su fafata da Sudan ta kudu a ranar 17 ga watan Augasta.
Sannan zasu murza leda da Kenya a ranar 19 ga watan Augasta, kana zasu karkare wasansu da Djibouti a ranar 22 ga watan Augasta. Rukunin A ya kunshi kasar Tanzania mai masaukin baki sai Rwanda, Burundi, Somalia, da Sudan.
Kungiyoyin wasannin shiyyar CECAFA zasu fitar da kungiyoyi biyu daga shiyyar wadanda zasu halarci gasar ta 2019. Tanzania ta riga ta tsallake sharer fagen shiga gasar a matsayinta na mai karbar bakuncin gasar ta 2019 AFCON U-17. Kungiyoyin wasa uku dake kan gaba a gasar ta 2019 AFCON U-17 sune zasu shiga gasar share fagen shiga gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 wato FIFA U-17 a kasar Peru a 2019.(Ahmad Fagam)