in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Leicester City ta kulla yarjejeniya da Ghezzal daga Monaco
2018-08-08 17:45:46 cri
Dan wasan kasar Algeria winger Rachid Ghezzal ya bar kulob din Ligue 1 Monaco zuwa Premier League a bangaren Leicester City, dukkannin kungiyoyin wasan biyu sun sanar da hakan ne a ranar Lahadi.

Winger mai shekaru 26 a duniya, ya kulla yarjejeniyar kwantiragi ta shekaru 4 da sabon kulub din, sai dai ba'a bayyana farashin da aka sayi dan wasan ba.

Zai hadu da manajan kulub din na Leicester City Claude Puel, wanda shine mai kula da kwalejin bada horo ta Lyon inda winger ya samu cigaba ta bayan da ya samu horo a kwalejin.

"Ina matukar farin ciki da na samu zuwa wannan waje. Nasan kociyan tun a Lyon kuma wannan wajen nake son zuwa. Kungiyar wasa ce mai kyau kuma tana da babban buri. Leicester City tana da manyan 'yan wasa kuma ina fatan zasu samu kyakyawar nasara a kakar wasan" inji Ghezzal bayan ya rattaba hannu kan kwantiragin.

Ghezzal ya halarci kwalejin Lyon a lokacin yana da shekaru 12 a duniya, kuma ya sanya hannu kan kwantiraginsa ta farko a matsayin kwararren dan wasa a shekarar 2010. Winger ya shafe shekaru biyu a kwalejin Lyon kafin daga bisani ya samu karin girma zuwa kulob din farko. ya samu babban matsayi ne a watan Oktoban shekarar 2012 a kungiyar wasan UEFA Europa League.

"Ya kasance a matsayin wani cigaba ne ga kungiyar wasan mu wanda zai kawo mana sabbin dabaru, zai kara bada muhimmanci a kakar wasanninmu. Nasan kwarewarsa tun a kwalejin Lyon, a lokacin yana makaranta, kuma ina son zan sanya ido don ganin yana horas da kansa da kansa a wasannin Premier League," Puel ya bayyana hakan ne game da batun sanya hannun da yayi a kwanan nan.

Ghezzal ya bayyana a wasansa a kungiyar wasan Algeria a watan Maris na shekarar 2015 kana yayi wasa a dukkan matakan wasannin kungiyar a gasar cin kofin kasashen Afrika a shekarar 2017. Zai kasance sanya hannunsa a kulob Leicester City karo na biyar kenan a kakar wasannanin lokacin zafi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China