in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin ya ba da lambobin yabo 40 ga wadanda suka karfafa alakar Sin da Uganda
2018-08-30 10:41:28 cri

Kimanin 'yan kasar Uganda 40 da suka yi rubuce rubucen labarai da suka daga matsayin dangantakar Sin da Uganda suka samu lambar yabo daga ofishin jakadancin kasar Sin dake Uganda.

Labaran wadanda aka wallafa su a wata jaridar kasar mai suna New Vision, tun daga watan Aprilun wannan shekara sun ja hankalin masu sha'awar shiga gasar da aka yiwa taken "My China Story" wato "labarina game da Sin" wanda ofishin jakadancin Sin dake Uganda ya dauki nauyi.

Daga cikin labaran da aka rubuta, akwai na wasu daliban jami'a da suka samu damar guraben karatu a fannoni daban daban a kasar Sin, da 'yan kasuwa wadanda suka amfana daga takwarorinsu na kasar Sin, da wadanda suka samu guraben ayyukan yi wadanda rayuwarsu ta sauya tun bayan da suka fara amfana da albashi mai kauri daga kasar Sin.

Chu Maoming, jami'in ofishin jakadancin Sin a Uganda, ya ce mutane 5 dake sahun farko da suka samu nasara, za'a dauki nauyinsu su ziyarci kasar Sin a watan Nuwamba domin su kara ilmi game da irin ci gaban da Sin ta samu, da kuma yadda yanayin al'ummar Sinawa yake.

Ya kuma sanar da cewa, tuni ofishin jakadancin ya riga ya kammala shirye shiryen karshe na samar da takardun visa ga tawagar 'yan kasar Uganda wadanda za su halarci taron kolin FOCAC na Beijing. Kuma shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ne zai jagoranci tawagar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China