in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samar da guraben aiki sama da 16,500 a Uganda a 2017
2018-01-31 09:38:05 cri

Jakadan kasar Sin a kasar Uganda Zheng Zhuqiang ya bayyana cewa, wasu ayyukan da kasar Sin ta samar da kudaden aiwatar da su a Uganda da yawansu ya kai 53, sun samar da guraben aikin yi kimanin 16,511 ga al'ummar kasar a cikin farkon watanni 11 na shekarar 2017, kana yawan ciniki tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka miliyan 750 a cikin wannan wa'adin.

Zheng ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Kampala, babban birnin kasar Uganda, a lokacin da yake jawabi ga dubban Sinawa mazauna kasar a gun bikin taya murnar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa wadda ke tafe a nan gaba.

A shekarar 2017, kasashen Sin da Uganda sun samu gagarumin ci gaba ta fuskoki da dama da suka hada da kyautata mu'amalar tattalin arziki, da cinikayya da zuba jari, da raya al'adu, da musayar ilmi da baiwa gwamnati tallafi, in ji jakadan na Sin.

Kana ya buga misali da cewa, shekaru uku da suka gabata ne aka kaddamar da hadin gwiwa tsakanin kwalejin Confucius dake jami'ar Makerere ta Uganda da jami'ar Xiangtan ta kasar Sin, hakan ya kasance a matsayin babban misalin yadda aka samu zurfafa mu'amala tsakanin al'adun al'ummomin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China