in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda zai halarci taron kolin dandalin FOCAC a Beijing
2018-07-25 10:02:11 cri

Wani babban jami'in kasar Uganda ya fada a jiya Talata cewa, shugaban kasar Ugandan Yoweri Museveni zai halarci taron kolin dandalin hadin kan Sin da Afrika wato (FOCAC) dake tafe, wanda za'a gudanar a watan Satumba a Beijing, babban birnin kasar Sin.

Henry Oryem Okello, karamin ministan harkokin wajen kasar Uganda, ya bayyana hakan ne a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, shirye shirye sun yi nisa don halartar taron.

Okello ya ce, "Tabbas, an kammala komai. Zan iya tabbatar da cewa shugaba Museveni zai ziyarci kasar Sin don halartar taron kolin FOCAC. Yanzu muna ci gaba da yin shiri zuwan shugaban".

Museveni zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afrika domin lalibo hanyoyin karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika.

Zheng Zhuqiang, jakadan kasar Sin a Uganda, a watan da ya gabata ya shedawa 'yan jaridu cewa, a lokacin taron kolin, za'a sanar da sabbin matakan yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu wadanda za su samar da wasu damammaki masu cike da ma'anar tarihi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China