in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ba da gudunmuwar magunguna ga asibitin kawance ta Uganda
2018-08-10 10:49:37 cri

Kasar Sin ta ba da gudunmuwar magunguna da kayayyakin kula da lafiya ga asibitin kawance ta kasar Sin da Uganda dake birnin Kampala.

Jakadan kasar Sin a Uganda, Zheng Zhuqiang ne ya mika magunguna da kayayyakin da darajarsu ta kai dala 70,000 ga ministar lafiya ta kasar Ruth Aceng.

Zheng Zhuqiang ya ce, hadin gwiwa a fannin kiwon lafiyar al'umma na daga cikin manyan bangarori 10 na tsare-tsaren hadin gwiwar Sin da Afrika, kamar yadda aka bayyana yayin taron koli na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afrika da ya gudana a shekarar 2015 a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu.

Ruth Aceng, ta ce gudunmuwar za ta taimaka sosai wajen inganta kula da marasa lafiya a asibitin mai gadaje 100, wanda gudunmuwa ce daga gwamnatin kasar Sin.

Ta ce, gwamnatin kasarta na kokarin kammala shirye-shiryen fara gyarawa da fadada asibitin, inda a nan gaba, zai koma cibiyar kula da matsalolin kashi da ciwuka masu tsanani kamar irin na hatsari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China