in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda da dama
2018-08-25 15:37:50 cri

Rundunar sojojin Najeriya dake aikin kakkabe mahara a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin kasar, ta ce dakarun ta sun hallaka 'yan ta'adda masu tarin yawa, yayin wani sumame na baya bayan nan.

Kakakin rundunar tsaron kasar John Agim ne ya shaidawa manema labarai hakan a Gusau, fadar mulkin jihar ta Zamfara. Ya ce kimanin mutane 6,000 ne, wadanda a baya suka tserewa gidajensu, suka samu damar komawa. Agim ya ce, mutanen sun hada da na kauyukan kananan hukumomin Maradu, da Shinkafi da Zurmi.

Kaza lika jami'in ya kara da cewa, tuni mazauna wadannan yankuna suka komawa gonakin su, yayin da suka fara harkokin noma, da sauran nau'o'in hada hada tattalin arziki, kasancewar maharan dake addabar al'umma a yankunan sun rasa duk wata dama ta tada zaune tsaye.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China